Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, matasan da suka gudanar da juyi a kasar masar sun bukaci da a saka wa ranar juma'a mai zuwa ranar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Bahrain da ke neman sauyi na siyasa a kasar da suke fuskantar kisan kiyashi daga azzaluman mahukuntan kasar, da kuma gwamnatin wahabiyawan Saudiyya da kuma sarakunan Bahrain.
A daidai lokacin da mahukuntan kasar Bahrain da na Saudiyya suke yin amfani da karfin soji wajen murkushe yunkurin al’ummar kasar Bahrain, da ke neman a gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin mulki da siyasar kasar, ma’ikatar tsaron kasar Birtaniya ta fito karara ta furta cewa ita ce ta horar da jami’an sojin Saudiyya da suke murkushe zanga-zargar lumana da mutanen Bahrain suke gudanarwa.
Ma’aikatar tsaron kasar Birtaniya ta tabbatar da hakan ne a cikin wani rubutaccen bayani da ta aike wa majalisar dokokin kasar, bayan da ‘yan majalisar suka matsa lamba kan suna son su san rawar da da kasarsu take takawa dangane kisan gillar da ake yi kan fararen hula a Bahrain.
Tun kafin wannan lokacin dai wasu bayanan sirri sun tabbatar da cewa, maiaikatar tsaron kasar Birtaniya ta aike da wasu kwararru kan harkar soji a asirce zuwa kasar Saudiyya, inda suke horar da jami’an tsaron kasar da suka hada da sojoji da kuma 'yan sanda, kamar yadda hukumar leken asiri ta kasar Amurka CIA take horar da ma’aikatan hukumar leken asiri ta kasar Saudiyya.
Babbar manufar hakan dai ita ce bayar da kariya ga gidan sarautar Ali-Sa’ud da a halin yanzu ke fuskantar barazana ta siyasa da tsaro. Bayan da al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da zanga-zanga a ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata, domin neman mahukuntan kasar su gudanar da garanbawul a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, ma’aikatar tsaron Birtaniya ta horar da wasu sojoji na musamman a kasar Saudiyya, daga bisani kuma Saudiyya ta tura su cikin kasar Bahrain dauke da kayan yaki, da sunan kare masarautar kasar ta Bahrain daga boren al'ummar kasar.
800921