IQNA

Wasu 'Yan Majalisar Kasar Amurka Sun Bukaci Da A Kare Hakkokin Musulmi

17:45 - May 31, 2011
Lambar Labari: 2131748
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Amurka sun bukaci da a dauki matakan da suka kamata domin kare hakkokin musulmin kasar, bisa la'akari da yadda ake cin zarafinsu da danne hakkokinsu, da kuma nuna musu wariya a cikin dukkanin harkoki.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Amurka sun bukaci da a dauki matakan da suka kamata domin kare hakkokin musulmin kasar, bisa la'akari da yadda ake cin zarafinsu da danne hakkokinsu, da kuma nuna musu wariya a cikin dukkanin harkoki na kasar, wanda a cewarsu ya yi hannun riga da dokokin kasar.

a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wadda ta kebanci mata 'yan makarantun sakadandare na kasar, a babban dakin taruka na katafaren otel din nan na Kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wannan zaman taro za a horar da yaran ne kan muhimman hanyoyin koyon harda, inda suka hada da karatun da kuma tajwidi, inda malamai daga cikin makaranta da kuma wasu daga cikin alkalan da suka saba jagorancin gasar kur'ani ta kasa da kasa.

Za a fara gudanar da wani zaman taro na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wadda ta kebanci mata 'yan makarantun sakadandare na kasar, a babban dakin taruka na katafaren otel din nan na kasar da ke cikin birnin.

800872

captcha