Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wanda ya tarjama kwafin kur'ani mai tsarki a cikin harshen isfaniyanci ya bayyana cewa, da ganin ayoyin da ke cikin kur'ani dab a Allah ya safkar da su ba za a gane su, saboda kur'ani Allah ya kiyaye daga samun duk wata tawaye ko nakasu a cikin ayoyinsa baki daya kamar yadda ya sakar da su haka suke babu canji.
Mutumin mai suna Jafar Gonzalez, wanda ya kwashe tsawon shekaru yana karatu a babbar cibiyar ilimi ta birnin dan gane da lamurra da suka danganci addinin muslunci da kuma tarjamar littafai na ilmomin ya bayyana cewa, a koda yaushe kalamin Allah madaukakin sarki daban yake da kalamin waninsa, a kan haka fita daga kur'ani abu ne da a zahiri zai nuna ma mai tarjama abin da yake ciki.
Wanda ya tarjama kwafin kur'ani mai tsarki a cikin harshen isfaniyanci ya bayyana cewa, da ganin ayoyin da ke cikin kur'ani dab a Allah ya safkar da su ba za a gane su, saboda kur'ani Allah ya kiyaye daga samun duk wata tawaye ko nakasu a cikin ayoyinsa baki daya.
802287