Bangaren kasa d akasa, daya daga cikin fitattun malaman addini kuma masana daga kasar Burma Ali Muhammad ya bayyana cewa, marigayi Imam Khomeni ya yi amfani da salo na ilimi wajen shiryar da mutane zuwa ga sahihin tafarkin koyarwar addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo an bayyan acewa, daya daga cikin fitattun malaman addini kuma masana daga kasar Burma Ali Muhammad ya bayyana cewa, marigayi Imam Khomeni ya yi amfani da salo na ilimi wajen shiryar da mutane zuwa ga sahihin tafarkin koyarwar addinin muslunci wanda hakan kuma shi ne mabudin dukkanin nasarar da ya samu.
Malamin wanda daya ne daga cikin fitattaun malaman addinin Musulunci kuma masana a kasar Bama, ya bayyana cewa Imam Khomeini (RA) ya bayar da gudunmawa ga al'ummar muslumi, wadda har duniya ta nade ba za a taba mantawa da shi ba, domin kuwa ya kafa tafarki na yin aiki da koyarwar addinin muslunci tare da fadakar da al'ummar musulmi nauyin da ya rataya kansu.
Daya daga cikin masu halartar taron tunawa da zagayowar cika shekaru 22 da wafatin marigayi Imam Khomeini (RA) jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya bayyana cewa dukkanin ayyukan Imam sun ginu ne a kan koyarwar kur'ani mai tsarki.
803276