IQNA

Fara Taron Kasa Da Kasa Na Malaman Musulunci A Senegal

15:28 - June 07, 2011
Lambar Labari: 2134372
Bangaren kasa da kasa: an fara wani taron kasa da kasa a jiya sha shidda ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal day a kumshi malaman addinin musulmi.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa' an fara wani taron kasa da kasa a jiya sha shidda ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal day a kumshi malaman addinin musulmi.An fara gudanar da wannan taro ne da mi8salin karfe goma a gogon kasar ta Senegal a taron da aka bawa taken rawar da malamai musulmi ke takawa a cikin saue-sauyen da duniya ke fuskanta da kuma matsayinsu har ila yau an fara wannan taron ne tare da jawabin Abdallah Wade shugaban kasar ta Senegal. Kuma wannan taro shi kansa shugaban kasar ta Senegal ne ya dauki dawainiyar gudanar d ashi a matsayinsa na shugaban karba-karba na kungiyar hadin kan kasashen musulmi kuma taron za a ci gaba da gudanar da shi har zuwa gobe laraba sha takwas ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya. An samu halartar malamai dam asana da kuma marubuta da suka fito daga kasashen musulmi da wasu makobtaka da kasar ta Senegal.



803598
captcha