Bangaren siyasa da zamantakewa: Imam Khomeini ® yana haskaka fuskoki da matsayin jama'a kuma saukin kai da rashin girman kansa ne ya kara kusantar da shi da jama'a da kuma ya samu karbuwa da farin jinni a tsakanin jama'a.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa' Imam Khomeini ® yana haskaka fuskoki da matsayin jama'a kuma saukin kai da rashin girman kansa ne ya kara kusantar da shi da jama'a da kuma ya samu karbuwa da farin jinni a tsakanin jama'a. Muhammad Huseini Abidini mai kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a ketare a hukumar da ke kula da yada al'adun iran shi ne ya bayyana haka tare da Karin bayanin cewa; masana da daman e suka yi ittifaki kan wannan lamari na saukin kai da fahimtar jama'a da kuma kusanci da su da hakan ya taimaka matuka gaya wajan kara masa kwarjini da farin jinni a tsakanin jama'a a fadin duniya.
803781