IQNA

Kafa Kwamitin Kula Da Gasar Karatun Kur’ani Ta Duniya A Kuwait

17:42 - June 07, 2011
Lambar Labari: 2134444
Bangaren kasa da kasa, an kafa kwamitin da zai kula shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da za a gudanar a kasar Kuwait, wadda za ta kunshi matasa daga sassa daban-daban na kasashen larabawan yankin tekun fasha.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar al’anba an bayyana cewa, an kafa kwamitin da zai kula shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da za a gudanar a kasar Kuwait, wadda za ta kunshi matasa daga sassa daban-daban na kasashen larabawan yankin tekun fasha, kuma gasar za ta hada da bangaren hadisi.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Today.gm an bayyana cewa, za abude wata babbar cibiyar hardar kur’ani mai tsarki a birnin Crown na kasar Gambia, wanda cibiayar nan ta matasa musulmi ta kasar ta dauki nauyin ginawa da nufin bunkasa ayyukan kur’ani a kasar, musamman ma a tsakanin matasan kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na da matukar muhimmanci ga matasana kasar Gambia da aka san su da mayar da hankali a kan lamurran da suka danganci addini, ya ci gaba da cewa da dama daga cikin masu bindiddigin lamurra suna ganin cewa bude wannan cibiya zai kara karfin matasa masu sha’awar karatun kur’ani. 804034




captcha