Bangaren kasa da kasa, kwamitin koli na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Masar, ya bukaci jami’ar Azhar da ta saka fikhun mazbar iyalan gidan manzoa cikin manhajar darussanta, bisa la’akari da matsayin wannan mazhaba a cikin addini da kuma yawan mabiya tafarkinta akasar Masar da duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin al-tawafuq an bayyana cewa, kwamitin koli na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Masar, ya bukaci jami’ar Azhar da ta saka fikhun mazbar iyalan gidan manzoa cikin manhajar darussanta, bisa la’akari da matsayin wannan mazhaba a cikin addini da kuma yawan mabiya tafarkinta akasar Masar da duniya baki daya.
Shugaban kwamitin Sayyid Muhammad Duraini shi ne ya yi wannan kira, wanda kuma daya ne daga cikin fitattun masu fafutukar kare hakkokin al’ummar Masar tun lokacin mulkin fir’ananci na Husni Mubarak, a cikin bayanin nasa ya bukaci da a dauki matakn gaggawa wajen kawo karshen ayyukan wuce gona da irin na kungiyoyin salafiyya a kasar Masar.
Babban kwamitin koli na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Masar, ya bukaci jami’ar Azhar da ta saka fikhun mazbar iyalan gidan manzoa cikin manhajar darussanta, bisa la’akari da matsayin wannan mazhaba a cikin addini da kuma yawan mabiya tafarkinta a kasar Masar.
804007