IQNA

Fara Gudanar Da Zaman Taro Kan Alkalanci A Harkokin Kasuwanci A Muslunci

17:42 - June 07, 2011
Lambar Labari: 2134448
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular larabawa dangane da sanin mahangar muslunci dangane harkokin kudi da ma sauran batutuwa da suka shafi kasuwanci da lamurran banki, tare da halartar masana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Riyad cewa, an fara gudanar da wani zaman taro a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular larabawa dangane da sanin mahangar muslunci dangane harkokin kudi da ma sauran batutuwa da suka shafi kasuwanci da lamurran banki, tare da halartar masana daga kasashen muslmi da na larabawa.
ya nakalto wani rahoto daga shafin yanar gizo na islamtoday cewa, ma’atar kula da ayyukan leken asiri a haramtacciyar kasar Isra’ila ta bukaci da a daina watsa kiran salla a cikin masallatan birnin Qods, amma babban gamayyar kungiyoyi da cibiyoyin muslunci ta birnin Qods ta ki amincewa da hakan, tare da bayyana cewa wannan wani yunkuri na wuce gona da iri daga bangaren haramtacciyar gwamnatin yahudawa.
A bangare guda Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba a kan irin wannan ta’asa. 803901

captcha