IQNA

An Nada Sabon Shugaban Cibiyar Muslunci Ta Kasar Faransa

13:40 - June 08, 2011
Lambar Labari: 2134956
Bangaren kasa da kasa, mambobin cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar Faransa, dun gudanar da zaben sabon shugaban cibiyar, inda suka zabi Jamal Aubashu a matsayin sabon shugaban wannan cibiya ta mabiya addinin muslunci mazauna kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, mambobin cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar Faransa, dun gudanar da zaben sabon shugaban cibiyar, inda suka zabi Jamal Aubashu a matsayin sabon shugaban wannan cibiya ta mabiya addinin muslunci mazauna kasar ta Faransa.

Wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar alkhalij cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan makomar musulmi a siyasar duniya, wanda za a gudanar a katafaren otel din nan na Shangrila da ke birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar masana daga kasashen musulmi da na larabawa.

Wannan zaman taro dai yana da matukar muhimmanci wajen sanin muhimman abubuwan da ya kamata mabiya addinin Musulunci su mayar da hankali kansu, musamman ma ta fuskacin matsayinsu a siyasr duniya da tattalin arziki, sauran lmaurra da suka danganci amantakewarsu a nan gaba.

804588
captcha