Bangaren kasa da kasa: da dama daga cikin kafafen watsa labarai na yammacin Turai karkashin kutse da matsin lambar yahudawan sahayoniya da Haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ta yada farfagandar batanci da dashe hasken Imam Khomeini ® da kuma tunani da nazarinsa amma a cikin shekaru ashirin da biyu da rasuwar sa sun kasa cimma manufarsu kuma tunani da tafarkinsa zai kara yaduwa yak e yi a fadin duniya.