IQNA

An Fara Gudanar Da Taro Karo Na Bakwai Na Tattalin Arziki Musulmi

Bangaren kasa da kasa; a ranar sha bakawi ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a garin Wife babban birnin kasar Kazakistan aka fara gudanar da taro karo na bakwai na kungiyoyin tattalin arziki na duniyar musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar sha bakawi ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a garin Wife babban birnin kasar Kazakistan aka fara gudanar da taro karo na bakwai na kungiyoyin tattalin arziki na duniyar musulmi. Mahalarta wannan taro suna tattaunawa ne kan hanyoyin day a kamata su kara habakawa da kuma inganta harkokin da sukashafi tattalin arziki a tsakanin kasashen musulmi tare da masanyar dabarun yin hakan yayin da a daya bangare kuma za su yi nazari kan hanyoyin day a dace su bi da za su taimaka wajan magance irin matsalolin da suke fuskanta a wannan bangare na tattalin arziki.

804331