Bangaren kasa da kasa: a gobe ne ashirin da uku ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya a garin Rabat babban birnin kasar Marokko za a gudanar da wani taro da zai yi nazari da bincike kan muhimmiyar rawar da matasa ke takawa a duniya wajan kare hakkin dan adam a duniyar musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a gobe ne ashirin da uku ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya a garin Rabat babban birnin kasar Marokko za a gudanar da wani taro da zai yi nazari da bincike kan muhimmiyar rawar da matasa ke takawa a duniya wajan kare hakkin dan adam a duniyar musulmi.Kungiyar Esesco da ke kula da bangaren ilimi da al'adu a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya wannan taro a daidai lokacin da bangaren zartar na wannan kungiya ya cika shekaru talatin da biyu da kafa shi da kuma taron a wannan karo ya zo a daidai lokacin da wasu kasashen larabawa ke fuskantar sauye sauye da boren kawo sauyi a siyasar kasashen daga matasansu.
806245