IQNA

Za A Bude Wani Baje Kolin Kayan Addinin Muslunci A Birnin London

18:42 - June 15, 2011
Lambar Labari: 2138978
Bangaren kasa da kasa, ana shirin bude wani baje koli na kayan muslunci da suka hada littafai da kuma abubuwan da ke nuni da matsayin ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa abirnin London.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sharq akl-ausat an bayyana cewa, ana shirin bude wani baje koli na kayan muslunci da suka hada littafai da kuma abubuwan da ke nuni da matsayin ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.
A bangare guda kuma a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka gabata.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
808595


captcha