Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci a kasar Masar Mahmud Izzat ya bayyana cewa, komawa zuwa ga koyarwar addinin muslunci da kuma fahimtar koyarwar wannan addini mai tsarki shi kadai ne hanyar fahimtar sahihiyar koyarwar addini ne.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alwafd ta kasar Masar cewa, daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci a kasar Masar Mahmud Izzat ya bayyana cewa, komawa zuwa ga koyarwar addinin muslunci da kuma fahimtar koyarwar wannan addini mai tsarki shi kadai ne hanyar fahimtar sahihiyar koyarwar addinin musulunci.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, Mgr Podvin babban mai magana da yawun kwamitin anyan malaman addinin kirista a kasar Faransa ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar take tafiyar da siyasarta kan mabiya addinin muslunci kuma marassa rinjaye a kasar,inda ake nuna musu banbanci na zahiri.
Ikmaluddin Auglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bayyana cewa, kungiyar za ta gudanar da wani zaman taro kan karuwar kymar musulunci a cikin wasu kasashen yammacin turai, inda za a tattauna dalilan hakan da kuma matakan da za a dauka domin kawo karshen wannan matsala da take fuskantar musulmi a wannan nahiya.
808458