Bangaren kasa da kasa, babbar tashar nan da ke watsa shirye-shiye kan kur’ani mai tsarki a kasar Algeria za ta watsa wani shiri mai suna tajul kur’ani a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke zuwa, inda shirin zai kunshi karatu da kuma bayanai kan ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki daga bakunan malamai daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Darul imam an bayyana cewa, babbar tashar nan da ke watsa shirye-shiye kan kur’ani mai tsarki a kasar Algeria za ta watsa wani shiri mai suna tajul kur’ani a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke zuwa, inda shirin zai kunshi karatu da kuma bayanai kan ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki daga bakunan malamai daban-daban.
A bangare guda kuma a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka gabata.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba. 809343