Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da wani shiri na gyaran masallatai a wasu yankuna na kasar Saudiyya, kamar yadda ma’aikatar kula da aharkokin musulunci ta kasar ta sanar, duk kuwa da cewa shirin zai takaitu ne kawai a bangarorin da wannan ma’akata ta ware domin gudanar da wannan aiki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga wata jaridar kasar Saudiyya cewa, za a fara gudanar da wani shiri na gyaran masallatai a wasu yankuna na kasar Saudiyya, kamar yadda ma’aikatar kula da aharkokin musulunci ta kasar ta sanar, duk kuwa da cewa shirin zai takaitu ne kawai a bangarorin da wannan ma’akata ta ware domin gudanar da wannan aiki wata kila saboda wasu dalilai da ba ta bayyana ba.
Wasu rahotannin da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sharq akl-ausat an bayyana cewa, ana shirin bude wani baje koli na kayan muslunci da suka hada littafai da kuma abubuwan da ke nuni da matsayin ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.
A bangare guda kuma a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka gabata.
809267