Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na tunawa da ranar haihuwar Imam Ali dan Abu Talib (AS) a birnin Vienna na kasar Austria tare da halartar malamai da kuma masana kan harkokin addinin muslunci, inda aka yi bayani kan matsayin Amirul muminin da kuma darussan da za a dauka a rayuwarsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na na cibiyar muslunci ta kasar ta bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na tunawa da ranar haihuwar Imam Ali dan Abu Talib (AS) a birnin Vienna na kasar Austria tare da halartar malamai da kuma masana kan harkokin addinin muslunci, inda aka yi bayani kan matsayin Amirul muminin da kuma darussan da za a dauka a rayuwarsa mai albarka.
Imam Ali (AS) dai shi ne wanda ya gaji ilimin manzon Allah (SAW) wanda Allah madaukakkin sarki ya sanya shi ya zama khalifa bayan manzonsa, tare da gadamarsa da ilimin manzon Allah da na annabawa, shi ne mai shiryarwa zuwa ga sahihin tafarkin manzon Allah a bayansa, yin riko da koyarwarsa shiri ne yin riko da tafarkin manzon Allah (SAW) a rayuwa.
Gudanar da wani zaman taro na tunawa da ranar haihuwar Imam Ali dan Abu Talib (AS) a birnin Vienna na kasar Austria tare da halartar malamai da kuma masana kan harkokin addinin muslunci, inda aka yi bayani kan matsayin Amirul muminin da kuma darussan da za a dauka a rayuwarsa mai albarka.
809280