Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; hukumar da ke kula da yada ilimi da tarbiya da kuma yada al'adu a kungiyar hadin kan kasashen musulmi Esesco ta fitar da wani bayani da a ciki take yin Allah wadai da cin fuska da tona kabarin musulmi da kuma karuwar abubuwan nuna kama kan musulunci a kasar Britaniya. A yan shekarun nan a kasar Britaniya an samu karuwar cin mutunci da nuna wariya kan musulmi da addinin musuluni a kasar a misalance a shekara ta dubu biyu da goma miladiya an kai wa musulumi da guraren ibadarsu hari har sau dubu daya da dari biyu kuma wannan wani adadi ne mai ban tsoro da kuma yake nuni da yadda kamar addinin musulunci da musulmi ke karuwa a wannan kasa a maimakon ya ragu.
809901