Bangaren kasa da kasa:Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin dsa shidda ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya gana da Harman Van Rampi shugaban komitin kungiyar tarayyar Turai a birnin Bruxel fadar mulkin kasar Beljuim inda suka gudanar da tattaunawa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin dsa shidda ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya gana da Harman Van Rampi shugaban komitin kungiyar tarayyar Turai a birnin Bruxel fadar mulkin kasar Beljuim inda suka gudanar da tattaunawa.Jami'an guda biyu sun tattauna da yin nazari kan matsalalin da ke addabar kungiyoyin su biyu da kuma hanyoyin warware irin wannan matsaloli da kuma hanyar da za a kara kusanci tsakanin al'ummomin musulmi da na nahiyar Turai musamman sun yi tattaunawar kan harkokin siyasa da tattalin arziki da al'adu a kungiyar tarayyar Turai.
809919