IQNA

Taron Tattaunawa da fahimtar Juna Tsakanin Musulmin Kasar Faransa

15:46 - June 20, 2011
Lambar Labari: 2141342
Bangaren kasa da kasa: a karo na sha bakwai a jiya ashirin da tara ga watan khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Bourgogne na kasar Faransa aka gudanar da wani taron tattaunwa da fahimtar juna a ranar da aka bawa taken ranar sani tsakanin musulmi kasar Faransa.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na sha bakwai a jiya ashirin da tara ga watan khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Bourgogne na kasar Faransa aka gudanar da wani taron tattaunwa da fahimtar juna a ranar da aka bawa taken ranar sani tsakanin musulmi kasar Faransa. Musulmin sun gudanar da wannan taro ne kamar yadda suka saba inda musulmi ke taruwa a rana guda a wani guri na musamman domin yin nazari da bincike kan halin da suke ciki na rayuwa da zamantakewa da kuma halin tattalin arziki da al'adu da kuma yin dogon nazari kan ci gaban da suka samu ko kuma akasin haka ma'ana irin matsa lilin da suke fuskanta a rayuwa a tsakaninsu da kuma da sauran al'ummo da mabiya addinai daban daban a kasar ta faransa ko kuma nuna masu wariya da kama a bangaren sauran al'ummomi day an siya da kuma bangaren gwamnati da hanyar da za su bi domin magance irin wadannan matsaloli.



811005
captcha