Bangaren al'adu da fasaha; Farid Iftikhari mai kula da ofishin al'adu da yada al'adun jamhuriyar musulunci a kasar sabros a wani taron tunawa da ranar da a irinta ce aka aifi Imam Ali (AS) ya bayyana cewa; Imam Ali (AS0 shi ne jigo madogara da abin koyi ga mumunai ta fuskar tsoran Allah da sadaukarwa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Farid Iftikhari mai kula da ofishin al'adu da yada al'adun jamhuriyar musulunci a kasar sabros a wani taron tunawa da ranar da a irinta ce aka aifi Imam Ali (AS) ya bayyana cewa; Imam Ali (AS0 shi ne jigo madogara da abin koyi ga mumunai ta fuskar tsoran Allah da sadaukarwa. Kuma ta wannan falsafar ce mabiya tarikar shi'a suka bi wajan yada addinin musulunci da kuma karfafa shi kuma ya bayyana haka ne a ranar alhamis din da ta gabata ashirin da shida ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shamsiya tare da kawo hadisan Imam Ali (AS) amirul Mumunina da kuma bayyana falalarsa.
811978