IQNA

Son Aiki Da Adalci Na Daga Cikin Muhimman Abin Da Imam Ali (AS) Kebantu

Bangaren al'adu da fasaha; Huseini Saburi mai kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Zambiya a lokacin bukin tuni da zagayowar irin wannan rana ta Haifuwar Imam Ali (AS) imami na farko nay an shia'a ya bayyana cewa; adalci da son aikata adalci na daga cikin muhimman abubuwan da Imam Ali (AS) ya kebantu da shi da kuma ya aikata da bukatar a aikata.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Huseini Saburi mai kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Zambiya a lokacin bukin tuni da zagayowar irin wannan rana ta Haifuwar Imam Ali (AS) imami na farko nay an shia'a ya bayyana cewa; adalci da son aikata adalci na daga cikin muhimman abubuwan da Imam Ali (AS) ya kebantu da shi da kuma ya aikata da bukatar a aikata.A ranar ashirin da takwas ga watan Khurda shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a masallacin Imam Rida da ke birnin Luzaka aka gudanar da bukin raya wannan rana ta haifuwar imam Ali (AS) rana mai muhimmanci da kuma tattare da tarihi ya gabatar da jawabi mai gamsarwa da kuma ya yi bayani dalla-dalla kan abubuwan da imam Ali (AS0 ya kebantu da su da kuma ya sha bamban da waninsa har ila yau ya kawo misalign addu'ar kummel da abubuwan ma'anawiya da wannan addu'a ta kumsa.

811656