Bangaren siyasa da zamantakewa: mukaddashin mai shirye-shirye a ofishin magajin garin birnin Qum ya bayyana wajibcin sani da karfafa aiki tare a tsakanin Iran da Sudan kuma wannan na daya daga cikin lamrin day a zama wajibi a gudanar da taro mai muhimmanci tsakanin manazarta da bincike kan ilmomin musulunci Iraniyawa da kuma yan Sudan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; mukaddashin mai shirye-shirye a ofishin magajin garin birnin Qum ya bayyana wajibcin sani da karfafa aiki tare a tsakanin Iran da Sudan kuma wannan na daya daga cikin lamrin day a zama wajibi a gudanar da taro mai muhimmanci tsakanin manazarta da bincike kan ilmomin musulunci Iraniyawa da kuma yan Sudan.A jiya ne aka fara gudanar da wannan taro wato a ranar talatin ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma a wata tattaunawa da minister ya yi da manema labarai na Ikna a birnin Qum Said Rida Dahnad ministan al'adu na ksar Sudan ya bayyana cewa: matsayin ilimi da al'adu da ma'anawiya a birnin Qum mai tsarki ya wuce bada misali kuma kasancewar Fatima Ma'asuma a wannan birni ya haskaka birnin ga kuma masallacin Jamkaran da daruruwar cibiyoyin ilimi da bincike a fuskar ilimomin addinin musulunci da sanayyar halayyar dan adam har ila yau kasancewar manyan malamai maraji'ai a wannan birnin na daga cikin abubuwan da suka daukaka wannan birnin.
812023