IQNA

Jami’ar Azhar Ta Bukaci A Kafa Gwamnatin Da Ba Ta Addini Ba A Kasar Masar

14:41 - June 22, 2011
Lambar Labari: 2142749
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa abin da suke bukatar gani shi ne an kafa gwamnati wadda ba ta addini ba a kasar Masar, bisa la;akari da cewa kasar tana mabiya addinai daban-daban da suke zaune lafiya tare da fahimatr juna a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AFP an bayyana cewa, babban malamin jami’ar Azhar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa abin da suke bukatar gani shi ne an kafa gwamnati wadda ba ta addini ba a kasar Masar, domin kuwa kasar tana da mabiya addinai daban-daban da suke zaune lafiya tare da fahimatr juna a tsakaninsu tun tsawon zamuna masu yawa.
Malaimin ya ci gaba da cewa babban abin fata shi ne a ga cewa an kafa gwamnati da demokradiyya, wadda za ta kare hakkokin dukkanin al’ummar kasar Masar, tare da gudanar da ayyukan gina kasa da al’umma, wanda acewarsa hakan shi ne zaman lafiyar al’ummar Masar baki daya da sauran al’ummomin yankin.
Babban malamin jami’ar Azhar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa abin da suke bukatar gani shi ne an kafa gwamnati wadda ba ta addini ba a kasar Masar, bisa la;akari da cewa kasar tana mabiya addinai daban-daban da suke zaune lafiya tare da fahimatr juna a tsakaninsu tun zamun da suka gabata.
812601

captcha