IQNA

An Fara Fitar Da Mujallar Iman Ta hanayar Internet A Kasar Faransa

14:42 - June 22, 2011
Lambar Labari: 2142752
Bangaren kasa da kasa, an fara fitar da mujallar iman da musulmin kasar Faransa suke bugawa ta hanyar yanar gizo, da nufin kara bayyana wa sauran masu magana da harshen Faransanci magana hakikanin abin da addinin musulunci yake koyar da musulmi, sabanin abin da ake yadawa kansa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na imanemagazine an bayyan acewa, an fara fitar da mujallar iman da musulmin kasar Faransa suke bugawa ta hanyar yanar gizo, da nufin kara bayyana wa sauran masu magana da harshen Faransanci magana hakikanin abin da addinin musulunci yake koyar da musulmi, sabanin abin da ake yadawa kansa, wanda kuma ita mujallar farko ta internet da musulmin kasar Faransa suka fara fitarwa.
A wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin ayyukan da fadar vatican ta saba shiryawa tun lokacin tsohon paparoma na biyu, wanda ya sa hakan ya zama wani zaman taro na shekara-shekara da ta saba gudanarwa, tare da halartar masana da malamai daga sassa daban-daban na kasashen duniya, da suka hada kasashen larabawa da na musulmi.
812490
captcha