Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada masaniya kan sirar manzon Allah (SAW) ta kasa da kasa, ta gabatar da shawara ga ma’aikatar kula da harkokin ilimin kanan makarantun kasar, da nufin koyar da su sirarsa, ta yadda za su samu masaniya kan hakan ta hanya mai sauki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij an bayyana cewa, cibiyar yada masaniya kan sirar manzon Allah (SAW) ta kasa da kasa, ta gabatar da shawara ga ma’aikatar kula da harkokin ilimin kanan makarantun kasar, da nufin koyar da su sirarsa, ta yadda za su samu masaniya kan hakan ta hanya mai sauki, domin kaucewa mummnan tasirin kyamar addinin muslunci da ake sakawa cikin kwakwalen al’ummar turai musamman a wannan lokaci.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, ikmaluddin Auglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bayyana cewa, kungiyar za ta gudanar da wani zaman taro kan karuwar kymar musulunci a cikin wasu kasashen yammacin turai, inda za a tattauna dalilan hakan da kuma matakan da za a dauka domin kawo karshen wannan matsala.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, Mgr Podvin babban mai magana da yawun kwamitin anyan malaman addinin kirista a kasar Faransa ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar take tafiyar da siyasarta kan mabiya addinin muslunci kuma marassa rinjaye a kasar,inda ake nuna musu banbanci na zahiri. 812416