IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Tashar Aljazeera A Mataki Na Karshe

13:56 - June 23, 2011
Lambar Labari: 2143129
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a mataki na karashe na gasar karatun kur'ani mai tsarki na tashar Aljazeera, wadda za agudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar wakilan makarantun kur'ani mai tsarki na kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta kanann yara ta aljazira cewa, za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a mataki na karashe na gasar karatun kur'ani mai tsarki na tashar Aljazeera, wadda za agudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar wakilan makarantun kur'ani mai tsarki na kasar baki daya, gami da kuma masana da malaman makarantu.

Rahoton ya ci gaba da cewa wannan zaman gasar karatun kur'ani shi ne na karshe a cikin dukkanin zaman da aka yi a lokutan baya, kuma da zaran an kammala za a sanar da wadanda suka nuna kwazo tare dab a su kyautuka na musamman, domin kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da gudanar da ayyuka na ci gaban karatun kur'ani mai tsarki.

Gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a mataki na karashe na gasar karatun kur'ani mai tsarki na tashar Aljazeera, wadda za agudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar wakilan makarantun kur'ani mai tsarki na kasar, wanda hakan zai bayar da damar kara bunkasa lamurran kur'ani a yankin.

813373

captcha