Bangaren siyasa da zamantakewa, kasar Malazia ta samu lambar yabo ta kasa mafi samun bunkasar harkokin kasuwanci a duniya daga cikin kasashen musulmi, tare da samun ci gaba da fuskar harkokin kudi da bankuna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kasar Malazia ta samu lambar yabo ta kasa mafi samun bunkasar harkokin kasuwanci a duniya daga cikin kasashen musulmi, tare da samun ci gaba da fuskar harkokin kudi da bankuna musamman ma bankin muslunci.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar hadin kankasashen musulmi ta OIC an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar turkiya, wanda ya yi nazari kan hanyoyi da za abi wajen bunkasa harkokin ilimi a duniyar muslmi, ta yadda za asamu ci gaba ta wannan fuska daida da sauran kasashen da suka samu ci gaba a duniya.
A wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
812843