IQNA

Za A Gudanar Da Taro Na Kasa Da Kasa Kan Ilimi Da Koyarwar Musulunci A Jamus

19:10 - June 23, 2011
Lambar Labari: 2143181
Bangaren kasad a kasa, za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan matsayin ilimi da kuma koyarwa a cikin addinin muslunci a kasar Jamus, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashen ketare.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na uni-goetting an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan matsayin ilimi da kuma koyarwa a cikin addinin muslunci a kasar Jamus, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashen ketare musamman kasashen musulmi da na larabawa.
Kasar Jamus dai na daya daga cikin nahiyar turai da ked a yawan mabiya addinin Musulunci, wadanda suke ganin cewa ya kamata gwamnatin kasar ta san da zamansu a matsayin mabiya wani addini na kasa a hukumance, lamarin da ke ci gaba da fuskantar turjiya daga mahukuntan kasar ta Jamus.
Gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan matsayin ilimi da kuma koyarwa a cikin addinin muslunci a kasar Jamus, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashen ketare, da suka hada da na musulmi da kuma na larabawa, har ma da wasu kasashen turai.
813481


captcha