Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Sabil an bayyana cewa, an bude wata cibiyar vkula da ayyukan kur'ani mai tsarki a birnin Manshia na kasar Jordan, wadda malaman addini da sauran masana na kasar suka halartaci bukin kaddamar da ita a jiya, kamar yadda wasu daga cikin malaman makarantun kur'ani mai tsarki na kasar suka halarta.
Rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
A bangare guda bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Auzbakistan ta gudanar da zama, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci mabiya addinin muslunci na kasar, musamman ma matsalolin da suke fuskanta ta fuskacin karancin ilimi da sauransu.
814123