Bangaren kasa da kasa, za afara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da hadisin ma’iki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsakaka a kasar Indonesia, tare da halartar makaranta da mahardata daga kashahen larabawa da na musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-riyad da ake bugawa akasar Saudiyya an habarta cewa, za afara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da hadisin ma’iki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsakaka a kasar Indonesia, tare da halartar makaranta da mahardata daga kashahen larabawa da na musulmi da wasu dag acikin kasashen gabacin nahiyar Asia.
Pira ministan kasar Malazia ya jaddada muhimmancin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron bude gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na Bernama cewa, pira ministan kasar Malazia ya jaddada muhimmancin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron bude gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin fadar mulkin kasar ta Malazia, dake samun halartar masana da kuma malaman addini.
814616