Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman karatun kur’ani mai tsarki a garin Nasiriyya da ke kasar Iraki domin tunaw ada babban malamin addini makarancin kur’ani mai tsarki na kasar Masar, Sheikh Abul Ainain, wanda Allah ya yi masa rasuwa a cikin wannan mako.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an habarta cewa, an gudanar da zaman karatun kur’ani mai tsarki a garin Nasiriyya da ke kasar Iraki domin tunaw ada babban malamin addini makarancin kur’ani mai tsarki na kasar Masar, Sheikh Abul Ainain, wanda Allah ya yi masa rasuwa a cikin wannan mako a birnin Alkahira.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar yaum Sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, an gudanar da zaman ta’aziyya na rasuwar babban malamin kur’ani kuma makaranci wato shekhul kurra na kasar Masar, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata, dukkuwa da cewa manyan malaman Azhar sun kauracewa janazarsa da kuma zaman ta’aziyar tasa.
Da dama daga cikin iyalan mamacin sun nuna matukar mamaki dangane da matakin da malaman jami’ar Azhar suka dauka na kaurace ma janazar shehin malamamin, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa harkokin kur’ani a akasar Masar, wanda ya kafa makarantun da suka samar da fitattun malaman kur’ani da makaranta da duniyar musulmi ke takama da su a halin yanzu a duniyar musulmi.
815274