Bangaren kasa da kasa, an kafa wani kwamiti na shirya tarukan addini da karatu da hardar kur'ani mai tsarki a garin Basara na kasar Iraki, musamman ma a cikin ranakun watan Ramadan mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana an bayyana cewa, an kafa wani kwamiti na shirya tarukan addini da karatu da hardar kur'ani mai tsarki a garin Basara na kasar Iraki, musamman ma a cikin ranakun watan Ramadan mai zuwa an shekarar bana, wanda ake sa ran za a samu gagarumin sauyi ta fuskar inganta tarukan kur'ani a kasar.
A wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
Gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar turkiya, wanda ya yi nazari kan hanyoyi da za abi wajen bunkasa harkokin ilimi a duniyar muslmi, ta yadda za asamu ci gaba ta wannan fuska daida da sauran kasashen da suka samu ci gaba na da matukar muhimmanci ga kasashen musulmi da na larabawa.
816049