Bangaren kasa da kasa:A ranar biyar ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a kasar Jodan aka fara gudanar da wani taro kan kafirta juna da kuma tasirin yin haka a duniyar musulmi kuma cibiyar tunani da al'adu na kasar ce ta shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: A ranar biyar ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a kasar Jodan aka fara gudanar da wani taro kan kafirta juna da kuma tasirin yin haka a duniyar musulmi kuma cibiyar tunani da al'adu na kasar ce ta shirya. Gudanar da irin wannan taro musamman a daidai wannan lokaci zai taimaka matuka gaya wajan inganta zamantakewa a tsakanin musulmi da akidu da mazhabobi da darikoki na musulmi musamman idan akla yi la'akari da cewa kafirta juna babu wani abu da yake haifarwa face kara kamar juna da nisantar juna da kuma rikici a tsakanin musulmi a duniya.
816173