IQNA

Masu Ra'ayin Addini A Maser Na Kokarin hana Tsayar Da Dan Takara Guda A Zaban Shugaban Kasar

Bangaren siyasa da zamantakewa: Abdul Mun'im Abu Fatuh tsohon mamba a kungiyar Ikwanul Muslim kuma daya daga cikin masu takarar neman shugabancin kasar ta Masar mai zaman kansa ya bukaci kungiyoyin musulmi da su ci gaba da kokarin hana tsayar dad an takara daya cilo.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Abdul Mun'im Abu Fatuh tsohon mamba a kungiyar Ikwanul Muslim kuma daya daga cikin masu takarar neman shugabancin kasar ta Masar mai zaman kansa ya bukaci kungiyoyin musulmi da su ci gaba da kokarin hana tsayar dad an takara daya cilo. Wasu masu sharhi kan zaben da kuma yanayin siyasa a kasar ta Masar bayan sauyi da kuma canje canjen da aka sami bayan boren day a tilastawa tsohon shugaban kasar ta Masar husni Mubarakk wasu na ganin yawan yan takara a wannan zabe zai taimakawa da fito da wasu yan siyasar kasar yayin da wasu kuma suke ganin hadewa da fitar dad an takara guda shi ne yafi dacewa da siyasar kasar a halin yanzu tare da gabatar da dalilai da sharhohi iri –iri.

816216