Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar da ke kula da ayyukan hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Karbala mai alfarma ta sanar cewa, za abude wani babban dakin ajiye kayan tarihi karkashin hubbaren mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, babbar cibiyar da ke kula da ayyukan hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Karbala mai alfarma ta sanar cewa, za abude wani babban dakin ajiye kayan tarihi karkashin hubbaren mai tsarki da ke samun ziyarar miliyoyin mutane a kowace shekara.
Wani rahoton kuma ya sheda cewa, kotun daukaka kara a kasar Iraki ta tabbatar da hukumcin kisan da aka yanke wa dan ta'addan nan da ya tayar da bom a hubbarorin Imamai Hadi da Askari (a.s) da ke garin Samarra na kasar Irakin shekaru biyar da suka gabata.
Majiyar kotun daukaka karar ta bayyana cewar kotun ta tabbatar da hukumcin da aka yanke wa Yusra Fadhil al-Turaiqi dan kasar Tunusiya da aka same shi da laifin tayar da bom a hubbarorin Imaman biyu a shekara ta 2006.
Jami'an tsaron kasar Iraki sun sanar da kame wannan dan ta'addan ne a wani samame da suka kai tungar 'yan ta'addan da ke birnin Bagadaza lamarin da ya yi sanadiyyar kashe abokansa 15 da kuma raunana Al-Turaiqi inda bayan binciken da aka gudanar aka tabbatar da hannunsa cikin harin ta'addancin da aka kai hubbarorin Imaman biyu (a.s).
816597