Bangaren kasa da kasa, an nada daya daga cikin fitattun malaman kur'ani na kasar Masar sheikh Tabalawi a matsayin shekhul kurra na kasar bayan rasuwar babban malamin na kur'ani na Masar Sheikh Abu Ainain, wanda Allah ya yi masa rasuwa amakon da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo cewa, an nada daya daga cikin fitattun malaman kur'ani na kasar Masar sheikh Tabalawi a matsayin shekhul kurra na kasar bayan rasuwar babban malamin na kur'ani na Masar Sheikh Abu Ainain, wanda Allah ya yi masa rasuwa a makon da ya gabata a birnin Alkahira.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kasar Malazia ta samu lambar yabo ta kasa mafi samun bunkasar harkokin kasuwanci a duniya daga cikin kasashen musulmi, tare da samun ci gaba da fuskar harkokin kudi da bankuna musamman ma bankin muslunci.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar hadin kankasashen musulmi ta OIC an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar turkiya, wanda ya yi nazari kan hanyoyi da za abi wajen bunkasa harkokin ilimi a duniyar muslmi, ta yadda za asamu ci gaba ta wannan fuska daida da sauran kasashen da suka samu ci gaba a duniya.
817428