Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaben majalisar mabiya addinin muslunci na Lugzamburg a mazabu biyar, domin fitar wadanda za su wakilci sauran musulmi a wannan kwamiti wanda shi ne ke gudanar da dukkanin lamurra da suka danganci mabiya addinin muslunci a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shoura an bayyana cewa, za a gudanar da zaben majalisar mabiya addinin muslunci na Lugzamburg a mazabu biyar, domin fitar wadanda za su wakilci sauran musulmi a wannan kwamiti wanda shi ne ke gudanar da dukkanin lamurra da suka danganci mabiya addinin muslunci a wannan kasa wadda daya ce daga cikin kasashen turai da suke da yawan mabiya addinin muslunci.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid an bayyana cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman sarakunan kasar gami da na kasar Saudiyya, tun daga lokacin da suka fara gudanar da gangamin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar.
Gudanar da zaben majalisar mabiya addinin muslunci na Lugzamburg a mazabu biyar, domin fitar wadanda za su wakilci sauran musulmi a wannan kwamiti wanda shi ne ke gudanar da dukkanin lamurra da suka danganci mabiya addinin muslunci a wannan kasa, yana da matukar muhummanci wajen fayyace wa musulmi makomarsu a dukkanin harkokin zamantakewa.
819038