IQNA

An Bude Cibiyar Kula Da Ayyukan Kur’ani Mai Tsarki Da Hardarsa A Birnin Dubai

16:22 - July 06, 2011
Lambar Labari: 2150211
Bangaren kasa da kasa, an bude wata babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki da harda a birnin Dubai na kasar haddadiyar daular larabawa, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa ayyukan ilimin kur’ani da fitar da sabbin hanoyin a wannan bangare.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar alkhalij an bayyana cewa, an bude wata babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki da harda a birnin Dubai na kasar haddadiyar daular larabawa, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa ayyukan ilimin kur’ani da fitar da sabbin hanoyin a wannan bangare mai matukar muhimmanci.
Bayanin ya ci gaba da cewa daya daga cikin muhimman ayyukan wannan cibiya sun hada da samar da makarantu na koyar da karatun kur’ani mia tsarki, da hakan zai shafi kira’a d akuma tajwidi, sai kuma bangaren harda, ta yadda za a kasa bangarorin zuwa matakai daidai kokarin dalibai.
Bude wata babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani mai tsarki da harda a birnin Dubai na kasar haddadiyar daular larabawa, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa ayyukan ilimin kur’ani da fitar da sabbin hanoyin a wannan bangare, na da matukar muhimmanci.
820502

captcha