Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd an bayyana cewa, manyan jami’ai da malamai a babbar jami’ar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar sun amince da kafa wata babbar cibiya tarjama rubuce-rubucen da aka yi a cikin addinin muslunci a zamunan da suka gabata da ma sauran zamunan da suka biyo baya.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Express Tribune an bayyana cewa, ana nuna wani dadden kwafin kur’ani mai tsarki a birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda ya kunshi matani kur’ani na larabci da kuma tarjamar wasu bangarori a cikin harshen da ake magana da shi a kasar tsawon zamunna da suka gabata.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
Manyan jami’ai da malamai a babbar jami’ar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar sun amince da kafa wata babbar cibiya tarjama rubuce-rubucen da aka yi a cikin addinin muslunci a zamunan da suka gabata da ma sauran zamunan da suka biyo baya da kuma na wannan zamini.
820429