IQNA

Tarukan Bayar Da Horo Na Hardar Kur'ani Mai Tsarki Ga Mata A kasar Saudiyya

11:40 - July 07, 2011
Lambar Labari: 2150388
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wasu tarukan bayar da horo mata masu sha'awar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya, shirin da babbar cibiyar nan mai kula da ayyukan alkhairi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wasu tarukan bayar da horo mata masu sha'awar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya, shirin da babbar cibiyar nan mai kula da ayyukan alkhairi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Jidda babbar cibiyar harkokin tattalin arzikin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri ya samu karbuwa matuka daga mata masu sha'awar hardar kur'ani, kuma za a gudanar da shi ne har tsawon watanni biyu a jere, wato a hutun bazarar shekarar da muk ciki, ba'ada bayan haka kuma shirin zai hada da koyar da su yadda za su aikata koyarwar kur'ani a acikin dukkanin harkokinsu na rayuwa.

Gudanar da wasu tarukan bayar da horo mata masu sha'awar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya, shirin da babbar cibiyar nan mai kula da ayyukan alkhairi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wanna bazaar.

820967


captcha