IQNA

An Gudanar Da Babbar Gasar Karatun Kur'ani Ta Internet A Saudiyya

13:30 - July 09, 2011
Lambar Labari: 2151191
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar kula da ayyukan alkhairi ta kasar Saudiyya ta gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar internet, inda aka shiga gasar da yaruka daban-daban da suka hada da larabci da kuma turancin ingilishi da kuma harshen urdu.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shams cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan alkhairi ta kasar Saudiyya ta gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar internet, inda aka shiga gasar da yaruka daban-daban da suka hada da larabci da kuma turancin ingilishi da kuma harshen urdu da ma wasu sauran yaruka.

A wata zantawa da ya yi da daya daga cikin mahalarta gasar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a abirnin Tehran, kuma wand aya wakilci kasar Tunisia a gasar Muhammad Awani ya bayyana cewa, , an kara samun gagarumin ci gab ata fuskacin ayyukan kur'ani mai tsarki a kasar Tunisia bayan faduwar shugaban mulkin kama karya na kasar Zainul abiding Bin Ali, wanda hakan ke nuni da irin yadda aka takura musulmi a kasar da suke da sha'awar karatu da hardar kur'ani mai tsarki, wanda daya ce daga cikin kasashe.

Bayanin ya ci gaba da cewa, yanzu haka akwai dubban matasa da suka shiga cikin shirye-shirye da wasu kungiyoyi suke yin a fadada karatu da hardar kur'ani a kasar, inda suke samun horo da kulawa daga cibiyoyin da ake ta kafawa domin gudanar da irin wadannan ayyuka a fadin kasar baki daya.

821875



captcha