Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin wadanda suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki karo na ashirin da takwas sun bayyana a cikin rauni, akan haka yana da kyau a kafa wani kwamiti da zai gudanar da zama da kuma binciken dalilan hakan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da yada daga cikin alkalan da suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani ta kasar Iran ta kasa da kasa Abdulfattah Darudi ya bayyana cewa, wasu daga cikin wadanda suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki karo na ashirin da takwas sun bayyana a cikin rauni, akan haka yana da kyau a kafa wani kwamiti da zai gudanar da zama da kuma binciken dalilan hakan domin kawo karshen wannan matsala.
Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shams cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan alkhairi ta kasar Saudiyya ta gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar internet, inda aka shiga gasar da yaruka daban-daban da suka hada da larabci da kuma turancin ingilishi da kuma harshen urdu da ma wasu sauran yaruka.
A wata zantawa da ya yi da daya daga cikin mahalarta gasar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a abirnin Tehran, kuma wand aya wakilci kasar Tunisia a gasar Muhammad Awani ya bayyana cewa, , an kara samun gagarumin ci gab ata fuskacin ayyukan kur'ani mai tsarki a kasar Tunisia bayan faduwar shugaban mulkin kama karya na kasar Zainul abiding Bin Ali, wanda hakan ke nuni da irin yadda aka takura musulmi a kasar da suke da sha'awar karatu da hardar kur'ani mai tsarki, wanda daya ce daga cikin kasashe.
821865