Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Bahrain, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar, a masallacin Abdulrahaman Ajur a birnin Hamad na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizona BNA an bayyana cewa, za a gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Bahrain, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar, a masallacin Abdulrahaman Ajur a birnin Hamad na kasar ta Bahrain.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan gasa, duk kuwa da halin da kasar take ciki na rikici, sakamakon yin amfani da karfi da mahukuntan kasar suke yi wajen murkushe masu gudanar da zanga-zangar lumana ta neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar da ke bin tarin fir'ananci na mulukiya.
Gudanar da wannan gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Bahrain, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar, a masallacin Abdulrahaman Ajur a birnin Hamad na kasar., na da matukar muhimamnci a wannan lokaci, domin tabbatar da hadin kan al'ummar kasar masu fuskantar zalunci da danniya.
823021