Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta mata a kasarBurnei, kuma an girmama dukkanin wadanda suka shiga gasar, kamar yadda aka bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Brunei online an bayyana cewa, an kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta mata a kasarBurnei, kuma an girmama dukkanin wadanda suka shiga gasar, kamar yadda aka bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a yayin gudanar da wannan gasa.
Wannan gasa dai tana cikin irinta da aka saba gudanarwa a kasar kowace shekara, musamman a lokutan watan Ramadan yake karatowa, domin zama cikin shirin fuslatar sauran gasar da za a gudanar a cikin watan mai albarka, inda akasarin mutanen kasar sukan mayar da hankalinsu kan lamurra da suka shafi kur'ani mai tsarki.
An fara karatun kur'ani mai tsarki na khatamar kur'ani a kasar Burnei wanda matasa da kuma daliban makarantun sakandare na kasar suke gudanarwa, tare da halartar jami'ai daga ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar.
kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta mata a kasarBurnei, kuma an girmama dukkanin wadanda suka shiga gasar, kamar yadda aka bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo zai kara karfafa gwiwar masu sha'awar shiga irin wannan gasa a nan gaba.
822881