IQNA

Baje Kolin Zane Zane Na Musulunci A Kasar Indiya

Bangaren al'adu da fasaha; an fara gudanar da baje kolin zane-zane da rubuce-rubuce mai taken musulunci da ofishin da ke kula da yada ilimi da tarbiya a kasar Indiya ya shirya a karamar jami'a ta fasaha da ke birnin Dahli na kasar ta Indiya.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an fara gudanar da baje kolin zane-zane da rubuce-rubuce mai taken musulunci da ofishin da ke kula da yada ilimi da tarbiya a kasar Indiya ya shirya a karamar jami'a ta fasaha da ke birnin Dahli na kasar ta Indiya. An fara wannan baje kolin net un ranar sha shida ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma an farawa ne da safe har zuwa karfe shidda na yamma inda aka samu halartar jakadun kasashen waje da ke zaune a kasar ta Indiya misali jakadan kasar malaishiya DT Singh Sang day a halarci gurin da ake gudanar da wannan baje kolin.

822862