Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a yau ne aka fara gudanar da wani taro day a kumshi bincike da nazari kan kisan gillar da aka yi wa musulmi a Sarbanistan kuma an samu halartar masana da kwararru da marubuta da kuma manazarta.Da misalign karfe tara na safe a gogon kasar ne a babban dakin gudanar da taro na profesa Salimi a jami'ar Amir kabir aka fara wannan taro.kuma masana daga yankin da sauran kasashe na duniya sun fara nazari da bincike kan kisan gillar da aka yi wa musulmi da kuma matsalolin zamantakewar cikin gida a kasar da yankin da kuma na kasa da kasa da yadda duniya da al'ummomin duniya da kungiyoyi na ciki da na kasa da kasa suka yi gum da bakinsu kan wannan lamari.
823069