IQNA

An Bukaci Kungiyar Tarayyar Turai Da Yanke Dangantaka Da Gwamnatin Isra’ila

14:18 - July 12, 2011
Lambar Labari: 2153317
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ya kirayi kungiyar tarayyar turai da ta yanke duk wata dangantaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, sakamakon ayyukan ta’addancin da take aikatawa kan al’ummar palastinu marassa kariya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na aljazeera cewa, babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar sheikh Ahmad Tayyib ya kirayi kungiyar tarayyar turai da ta yanke duk wata dangantaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, sakamakon ayyukan ta’addancin da take aikatawa kan al’ummar palastinu marassa kariya musamman ma a cikin shekarun baya-bayan nan inda ya kaddamar yakoki da kashe-kashe kansu.
A wani labarin kuma an gudanar da zaman ta’aziyya na rasuwar babban malamin kur’ani kuma makaranci wato shekhul kurra na kasar Masar, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata, dukkuwa da cewa manyan malaman Azhar sun kauracewa janazarsa da kuma zaman ta’aziyar tasa.
Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ya kirayi kungiyar tarayyar turai da ta yanke duk wata dangantaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, sakamakon ayyukan ta’addancin da take aikatawa kan al’ummar palastinu marassa kariya ba tare da an taka mata birki kan hakan ba.
823801


captcha