Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ya watsa rahoton cewa; a jamhuriyar Dagistan malamn addini musulunci sun gudanar da wani zaman fahimtar juna da kuma tattauanwa kan harkokin addini da kuma wasu lamura da suka shafi musulmin yankin inda kuma manya da fitattun mutanen yankin suka halarta.Wannan zama na tattaunawa yana da matukar muhimmanci musamman idan aka yi la'akari da abubuwann da ke faruwa a yankin da kuma rawar da malamai ke takawa a rayuwar yau da kullum ta musulmi da kuma irin taimakon da irin wannan tattaunawa ta malamai zai iya kawo wa a rayuwar musulmi da sauran mutanean da ke rayuwa da musulmin.
823296